• Labaran yau

  B-kebbi: Da sana'ar yankan kumba nike ciyar da iyalina mutum 9 - Sulaimana

  Malam Sulaimana Abubar wani mai sana'ar yankan kumba ne dan asalin garin Kangiwan Sambawa daga karamar hukumar Maiyama a jihar Kebbi yana da mata biyu da yara shida. Wannan bawan Allah yana ciyar da iyalinsa ne daga wannan sana'a.

  Sulaimana ya shaida mana cewa yakan shigo garin Birninin kebbi kullum daga kauyen su na Kangiwar Sambawa wanda yake biyan N300 kullum kasancewar kudin mota zuwa da dawowa daga kauyesu.

  Ya kara da cewa baya da wata sana'a bayan wannan yankan kumba amma a lokacin damana yakan taba aikin noma a kauyensu.Duk da yake yaran Sulaimana suna zuwa makaranta kamar yadda ya shaida mana,amma ya ce yakan sami kimanin N800 ne a kullum daga bisani ya cire N300 kasancewa kudin mota zuwa da dawowa daga garinsu. Daga karshe dai Sulaimana ya kan yi rayuwa kenan a kan N500 a kullum kasancewa shugaban iyali mai dauke da mutum tara mata biyu da yara shida .

  Malam Sulaimana ya roki gwamnatin jihar Kebbi ko masu abin hannu cewa su tallafa masa da kudi N5000 kacal domin a cewarsa kudin zai inganta sana'arsa sakamakon haka zai kara sayo kayan aikinsa.

  Labarin Malam Sulaimana ya zama ishara da izma akan bata gari wadanda suka bari zuciyarsu ta mutu ta hanyar kin tabuka wa rayuwarsu komi, ko samari da matasa da suke sace-sace da sunan rashin aikin yi.

  Daga Isyaku Garba

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta  Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: B-kebbi: Da sana'ar yankan kumba nike ciyar da iyalina mutum 9 - Sulaimana Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });