Gwamna Bagudu ya bukaci jama'a su kula da ayyukan da gwamnati ta yi masu

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya bukaci al'ummar jihar Kebbi su kasance masu kula da ayyuka da Gwamnati ta yi masu domin ganin aikin ya yi karko saboda a dade ana amfana da ayyukan.

Gwamna Bagudu ya bayyana wannan bukata ne a wani ziyarar gani da ido akan aikin ruwan sha da ya kai a ruggar Fulani a Hutawa kusa da garin Birnin kebbi.

Gwamnatin Abubakar Atiku Bagud ta dukufa wajen samar da hanyoyi a birane da karkara a fadin jihar Kebbi hadi da ababen more rayuwa kamar su rijiyoyin burtsatse,ilimi da inganta kiwon lafiya.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN