• Labaran yau

  Wajibi ne T.Y Danjuma ya nemi gafarar soji da yan Najeriya - Samaila Yombe

  Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai wanda tsohon soja ne mai mukamin Kanar (Colonel) ya bayyana bakin cikinsa akan kalamai da tsohon hafsan sojin Najeriya Gen.T.Y. Danjuma ya yi inda yace kalamai ne masu ban takaici.

  Col. Samaila Yombe wanda ya yi aiki da Gen. T.Y Danjuma a wurare daban-daban daga 1967 ya ce wajibi ne tsohon babban hafsan ya nemi gafarar 'yan Najeriya da sojin Najeriya gaba daya ganin  cewa yana da dama da zai iya bayar da shawara ga Manyan hafsoshin sojin Najeriya har ma da shugaban kasa amma bai yi haka ba.

  Col. Yombe ya ce abin takaici ne da nadama ganin cewa Gen. T.Y Danjuma ne yake zargin sojin Najeriya da hada baki da bata gari.Ya ce duk da yake bai kamata tsohon hafsan ya yi haka ba amma yana tuna ma Gen. T.Y Danjuma cewa dubban soji ne suka rasa rayukansu domin ceton martabar Najeriya kuma idan har Danjuma bai yaba masu ba bai kamata ya zarge su ba.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wajibi ne T.Y Danjuma ya nemi gafarar soji da yan Najeriya - Samaila Yombe Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });