An kama jami'ar NSCDC da mijin ta bisa zargin dillancin makamai

Rundunar yansanda a jihar Imo ranar Alhamis ta kama wata jami'ar rundunar NSCDC a jihar Imo tare da mijinta bisa zargin fataucin mugan makamai.Wadanda aka kama su ne Mrs.Gloria Ogbonna mai shekara 35 tare da mijin ta Chukwuma Ogbonna dan shekara 50 dukannin su yan asalin Umuoba Umopara ne a Umuahia ta yamma a ckin jihar Abia.

Kwamishinan yansanda na jihar Imo Chris Ezike ne ya gabatar da su ga manema labarai, ya kuma ce bincike ya nuna cewa ma'auratan ne ke ba kusurgumin dan fashi da yansanda suka kashe a bara E-Money makamai.

Makamai da yansanda suka samu yayin wani samame da SARS ta kai a gidan ma'auratan a Area 'N' rukuni na 4 a rukunin gidajen World Bank da ke Owerri sun hada da cartridge 79, harsashi 45 na 9mm,harsashi 118 na K2,bindiga kirar AK47 guda 47,Pistol guda 4 da revolver 17 da sauran kayaki da suka hada da kakin soja,na'urar hangen nesa da sauransu.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN