Ka san dalili da ke sa mata bijire zaman aure bayan sun haifi yara 3 ko 4 ?

Idan ka auri matar ka zai iya daukar lokaci mai tsawo kafin ka iya fahimtar cikakken halinta.Wata mace za ta iya boye halin ta kuma za ta yi iyakar ladabi da kyautatawa da za ta iya yi domin ta faranta maka rai.Amma bayan ta haifi kamar yara 3 zuwa 4 mugan halayen ta su fara bayyana.

A wani bincike da muka gudanar a ISYAKU.COM sakamakon binciken ya nuna cewa daga lokacin da wasu mata suka haifi yara 3-4 a lokacin ne suke jin cewa ai sun mallaki gida kuma ko da Maigida ya mutu ai sun ne suka mallaki gidan domin yayansu ne ke da gado.

Mata masu irin wannan tunani sukan yi zaton cewa ko da mai gida ya auro wata mace zai dauki shekaru kafin ta iya samar da yara 3-4 bale ta yi jayayya da ita akan mallakin gidan.

Sakamakon haka wasu mata sai su fara nuna rashin kunya da cin mutunci ga mazajen su.Wani lokaci ma har da wulakanci balle raini.

Sakamakon binciken mu ya nuna cewa irin wadannan mata basu yarda a kara masu kishiya kuma za su iya yin iyakar abin da za su iya yi domin ganin cewa sun hana maigida aniyarsa ta kara mata ta hanyar haddasa tashin hankali a cikin gidan.

Amma binciken namu ya nuna har ila yau cewa karin mata a irin wannan gida shine mafita domin a kashi 100 na irin gidaje da aka yi fama da irin wannan hali kashi 70 sun yi nadama kuma sun natsu bayan an kara masu kishiya yayin da kashi 30 suka karasa a rabuwar aure gaba daya.

Haka zalika babban burin irin wadannan mata shi ne su haddasa fitina da gangan domin maigida ya kasa jure wulakanci shi kuma ya sake ta domin ta kara gaba ta auri wani ta sake haihuwa domin ta haka sai ta tara wa kanta jari bisa tunani irin nasu.

Daga Isyaku Garba

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN