An gano gungun masu satar yara domin su sayar da su

Hukumar hana fataucin bil'adama ta kasa tare da hadin guiwa da rudunar tsaro ta DSS sun kama mutum 11 da ake zargi da fataucin yara a sassa daban-daban a jihar Anambra.Wadanda aka kama sun hada da Mata 8 da Maza 3 wadanda aka ce sun shahara wajen satar yara  a yankin yamma maso gabacin Najeriya har da Lagos da Abuja.

An ceto yara 3 wadanda shekarunsu ya kama daga wata 8 zuwa shekara 4 daga samamen jami'an. Daga cikin yaran da aka ceto har da yarinya yar shekara 2 da aka sato daga garin Lagos da wani yaro dan shekara 4 da aka sato daga Gudaba a babban birnin tarayya Abuja.
Har yanzu ba a gane iyayen yaro dan wata 8 da aka ceto ba yayin da Rosemary Okafor yar shekara 30 ta sayar da yaron ta guda daya cikin yaranta hudu a kan N350.000 wai tana son ta yi amfani da kudin ne domin ta biya wa sauran yaran 3 kudin makaranta.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN