Ziyarar jaje a Zuru- Samaila Yombe amini ne kuma masoyin Gwamna Bagudu - Sani Dododo

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya kai ziyarar jaje ga Masarautarsa ta Zuru inda ya duba irin barnar da gobara ta yi a  Masallacin tsohon Kasuwar Zuru daga bisani ya zarce zuwa garin Dabai inda a nan ma ya duba irin barnar da gobara ta yi a kasuwar.

A ziyara da ya kai a Fadar Sarkin Dabai wanda Kantoman Dabai kuma Sarkin Ushe ya wakilta Alh. Sani Dododo wanda shi ne shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Kebbi SEMA ya ambaci Matamakin Gwamnan jihar Kebbi Alh Samaila Yombe Dabai a matsayin "Masoyi kuma Aminin Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu".

Alh. Sani ya ce an rasa ran wani yaro dan shekara 7 sakamakon gobarar ta Dabai, haka zalika ya ce ana samun tashin gobara akalla guda goma a kowane rana a fadin jihar Kebbi a cikin lokacin hunturu wanda ke da alaka da sakaci da kone daji.

Ya kara da cewa wajibi ne a dauki kwakwarar mataki a kan wadanda ke haddasa wutar daji, ya ce watar daji tana halaka halittu da ke shimfide a cikin dajin bayan haka kuma yakan halaka wasu irin itatuwa da babu su a fadin jihar Kebbi face a kasar Zuuru. Daga karshe ya ce zai kai koke ga Gwamna Bagudu domin samun taimako.

Ya ce amma kafin wannan lokaci za a samar da taimakon gaggawa ga mutane da lamarin gobarar ta shafa washegari kafin samun taimakon Gwamna ya iso.

A nashi jawabi Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya jajenta wa jama'ar kasar Dabai bisa aukuwar wannan ibtil'i na gobara, ya kuma yi alkawari cewa zai gina manyan dakuna na kasuwa guda biyu a cikin kasuwar ta Dabai.

Dagab bisani tawagar ta kai gaisuwar ta'aziyya sakamakon rasuwar wani yaro a gobara dan shekara 5 a unguwar road block mai suna Isah wanda da ne ga Malam Musa.Daga bisani Yombe ya bayar da sadaka mai kauri ga uwayen yaron.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN