B-Kebbi: An daura auren Nura Mai Fata a babban Masallacin jihar Kebbi

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya halarci daurin auren Mataimakin shugaban 4+4 Alh. Nura Mai Fata Zuru da Halima Abubakar Zuru a matsayin wakilin ango wanda aka daura a babban Masallacin jihar Kebbi watau Central Mosque a cikin garin Birnin kebbi.

Babban Limamain  Masallacin ne Mal. Muhktar (Walin Gwandu) ya daura auren bayan Sallar Juma'a.

Daurin auren ya sami halarcin manyan yan siyasa na jam'iyar APC na jihar Kebbi, wadanda suka hada da Alh. Sani Dododo shugaban SEMA na jihar Kebbi, Alh. Sani Ka'ida dan Majalisan jihar Kebbi mai wakiltar Zur, Mataimakin shugaban jam'iyar APC na jihar Kebbi Alh. Abukakar Kana da sauran manyan 'yan siyasa.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN