• Labaran yau


  Zargi: Yadda dansanda ya harbe yaron mota a kan N100 - Hotuna

  Wani hoto da ke yawatawa a shafukan yanar gizo wadda ya samo asali daga shafukan kudancin Najeriya sun nuna hotuna da ake zargin cewa wani dansanda ne ya kashe wani yaron wata motar Tipa wadda ta dauko yashi sakamakon zafafar cacan baki a kan N100 ranar Juma'a.

  Shi dai dansandan da ake zargi da aikata wannan danyen aikin yana aiki ne a caji ofis na Okwelle a karamar hukumar Onuimo na jihar Imo.

  Bayanai sun nuna cewa wannan dansandan ya auna sa'a domin kadan ya rage shi ma a aika shi barzahu sakamakon fusata da jama'a suka yi a kan lamarin.
   
  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Zargi: Yadda dansanda ya harbe yaron mota a kan N100 - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama