Wani bayani mai inganci da muka samu ya nuna yadda Arewacin Najeriya ke fuskantar barazana daga cikin gida na kasancewa 'yan Arewa ne mafi koma baya wajen yawan wadanda suka yi rijistan Katin Zabe na kasa a hukumar Zabe.
Wani abun mamaki shi ne shi dai wannan katin zabe kyauta ake bayarwa, amma har yanzu tazara da da aka samu tsakanin yawan wadanda suka yi rijista daga kudancin Najeriya ya rinjayi yawan wadanda suka yi rijista a Arewacin Najeriya.
Kididdiga ya nuna cewa Arewacin Najeriya ya fi yawan al'umma amma sakaci na Malam dan Arewa shi kanshi barazana ne ga ci gaban Arewa a wajen zabe na kasa musamman zaben shugaban kasa.
Ya zama wajibi gwamnatocin Arewa su tashi tsaye domin fito da tsari da zai sa 'yan Arewa su yi wannan rijistan katin zabe mai matukar muhimmanci.
Wannan bayani ya fito ne daga hukumar zabe ta Najeriya INEC
Yawan wadanda suka yi rijistan katin zabe a yankunan Najeriya:
1). Kudu maso Kudu - 10, 676,957
2). Kudu maso Gabas - 8,146, 833
3). Kudu maso Yamma - 14, 220, 569
4). Arewa maso Gabas - 9, 325,647
5). Arewa ta Tsakiya - 11,157, 988
6). Arewa maso Yamma - 18, 033, 850
2). Kudu maso Gabas - 8,146, 833
3). Kudu maso Yamma - 14, 220, 569
4). Arewa maso Gabas - 9, 325,647
5). Arewa ta Tsakiya - 11,157, 988
6). Arewa maso Yamma - 18, 033, 850
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Tags:
LABARI