Yan kasuwa sun bukaci gwamnati ta kammala titin sabuwar kasuwar Zuru

Kungiyar yan kasuwa na kasar Zuru karkashin jagorancin Mataimakin shugaba Murtala Abdullahi tare da wasu jigogi a kungiyar sun kai ziyarar nuna goyon baya tare da godiya ga Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin  Sanata Abubakar Atiku Bagudu bisa sabon titin mota da Gwamnati ta yi a sabuwar kasuwar Zuru tare da rokon Gwamnati ta kammala sauran gurbi da ya rage na hanyar .

Sun kuma yi wa Gwamnati godiya bisa nagartaccen kokari da Gwamnati ta yi na dauke kasuwar daga tsohuwar kasuwa zuwa sabuwar kasuwa, haka zalika sun bukaci Gwamnati ta tallafa wa' yan kasuwa da suka gamu da karayar arziki sakamakon tashin tsohuwar kasuwar zuwa sabuwa.

A jawabinsa tun da farko Mataimakin shugaban jam'iyyar APC. na jihar Kebbi Alh. Abubakar Kana ya yi jawabin gabatarwa ne ga Mataimakin Gwamna.

A nashi jawabi,Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya nuna godiya bisa yadda' yankasuwar suka mutunta Gwamnati tare da rokon Allah ya kawo waraka ga wadanda suka sami karayar arziki. Ya kuma ce zai gabatar da koken nasu ga Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu.

Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban yan kasuwar Zuru,Mataimakin shugaban jam'iyar APC na jihar Kebbi Alh. Abubakar Kana, Shugaban karamar hukumar Zuru Alh. Muhammad Abubakar Kabir, shugaban yan kasuwa Alh.Usman Na Danko da shugaban Mata Hadiza Samaila.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN