Karanta yadda Kaka ta azabtar da jikoki domin ta kamu da cutar HIV

Wadannan yara sun sha azaba ne a hannun kakarsu wacce take saka adda a wuta bayan ya yi zafi sai ta zaro addan ta yi ta dukan wadannan yara Marayu 'yan shekara 13.5 da shekara 3 duk da yake tsohuwar da ke gana masu wannan azaba Kakarsu ce.

Yaran sun ce sun daina zuwa Makaranta a 2016 bayan rasuwar Mahaifiyarsu, kuma tun 2014 Mahaifinsu ya mutu.Sun kara da cewa Kakarsu tana tilasta su domin su amsa cewa su Mayu ne alhalin su ba Mayu bane.

Wata majiya ta ce tsohuwar tana dauke da cutar HIV wadda ta ta'allaka laifin kamuwarta da cutar akan Maitar yaran guda uku.

Wani Lauya mai kula da hakkin bil'adama Barr. James Ibor ya shigo cikin lamarin inda yake taimakawa domin ganin yaran sun sami adalci.

ASP Irene Ugbo wanda shi ne kakakin hukumar 'yansanda na jihar Cross Rivers ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce har yanzu 'yansanda na gudanar da bincike.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN