• Labaran yau


  Karamar hukumar Zuru za ta gina wa yan kasuwan Zuru ofis a cikin kasuwa

  Shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru a kudancin jihar Kebbi Alh. Muhammed Kabir Abubakar ya ce Majalisarsa za ta gina wa yan kasuwa ofis a sabuwar babban kasuwar garin Zuru hedikwatar Masarautar Zuru.

  Alh.Kabir ya yi wannan bayanin ne a ofishin Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai yayin da tawagar kungiyar 'yan kasuwar Zuru suka kai ziyara a ofishin Mataimakin Gwamna a Birnin kebbi ranar Laraba.

  Ya ce za'a yi amfani da kudin shiga da karamar hukumar ke samu ne domin a gina ofishin domin su ma yan kasuwa su amfana da Gwamnati.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karamar hukumar Zuru za ta gina wa yan kasuwan Zuru ofis a cikin kasuwa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama