Zamani ya canja haka zalika yadda ake tafiyar da rayuwa ya canja, a Duniyar mu ta yau amfani da wayar Salula ya zama wani abun ado kuma madogara ga tsarin sadarwar zamani cikin sauki.
Bayan samun wannan gagarumin ci gaba a rayuwa ta fannin sadarwa, bisa wannan tubali kuma aka sami mutane masu mugun nufi da ke iya amfani da fasahar zamai domin su yi satar sauraren zancen da kake yi da wani a wayar salularka.
Ga kadan daga yadda za ka iya ganewa tare da dakile ko wani yana satar sauraron zancen ka tare da wani yayin da kake zance tare da wanda ka kira ko ya kira ka.
1. Ka danna *#61# a wayarka wannan zai nuna maka ko an karkata zancen ka domin wani ya saurara ko akasin haka domin zai nuna Call forwarded ko akasin haka
2. Idan ya nuna Call forwarded to lallai ana sauraron wayarka idan kana magana a wayar Salularka.Sai ka danna ##21# wanda zai ba ka dama ka cire na'urar da ake sauraronka da shi daga lambar wayar da zai bayyana bayan ka danna lambobin nema na ##21#.
Saboda haka yana da kyau kowane mako ka duba wannan bayani sakamakon gurbacewar amana ko da a tsakanin jami'an tsaro ne ko wadanda kake zaton cewa abokananka ne.
Daga Isyaku Garba, Mawallafi, Sharhi da Nazari.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Tags:
FADAKARWA