• Labaran yau

  Wannan ne kwamandan SARS da Fulani suka kashe a Saki jihar Oyo

  Wannan bawan Allah ne ake zargin Fulani sun kashe shi a Saki na jihar Oyo ranar daren Talata. ASP Shehu Magu shi ne shugaban sashen SARS na hukumar yansanda a rundunar yansanda reshen Saki.

  Magu ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ke gudanar da aiki a gandun hanyar Saki-Ogbooro a Oke-Ogun na jihar ta Oyo.Rototanni sun nuna cewa akwai wani jami'in dansanda daya da ke aiki tare da hafsan shima Fulani sun kashe shi.

  Wani jami'in dansanda sashen bincike a jihar Oyo mai suna Dhammy Rehob ne ya wallafa hoton a yanar gizo inda ya yi wa mamacin addu'a.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Wannan ne kwamandan SARS da Fulani suka kashe a Saki jihar Oyo Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama