Zaben 2015: Inyamuri ne ke kalubalantar kujerar Gwamna Bagudu a Kotu !

Wannan lamarin kamar almara, wai yadda ta kasance a sahihancin yadda aka bari bango ya tsage Kadangare ya sami wurin shiga a kan neman Duniya....MULKI a jihar Kebbi.Hausawa sun ce babu ruwan Kifi da Kaska!...ka ji karfin hali. Ya kai dan jihar Kebbi wanda ke kaunarta da neman kare muradun ta, ko ka san cewa Inyamuri ne ke kalubalantar kujerar Gwamnan jihar Kebbi a kan zaben 2015,kujerar Sanata Abubakar Atiku Bagudu ?.

Abin da ban mamaki,shin kwangilar wannan Inyamuri aka yi domin wulakanta darajar jihar Kebbi ta hanyar yin amfani da shi ko kuma gazawa ne daga bangaren wadanda suka dauke shi kwangila domin ya yi wannan aiki?.

Yayin da jihar Kebbi da Sarakunan ta masu Alfarma suka karrama yan kabilar Inyamurai ta hanyar ba su sarautar gargajiya kamar Mukamin gargajiya na Dan jikan Gwandu da Mabudin Zuru duka Inyamurai ne aka  ba. Amma yan jihar Kebbi nawa ne aka ba sarautar gargajiya a kasar su ta Inyamurai?

Yayin da aka jiyo Gwamna Atiku Abubakar Baguda a kafafen labarai ya ce "za su kare kasancewar Najeriya kasa daya da digon jinin su na karshe" sai ga Inyamuri ya dukufa ka'in da na'in wai ala tilas Dan Bagudu bai cancanta ba a zabe da aka yi a jihar Kebbi wacce ba kasarsa ba bai taba zuwa jihar Kebbi ba amma wai shi ne ya shigar da kara akan lamarin jihar Kebbi har da takarkarewa ala tilas wai sai ya jagula kwanciyar hankali a jihar Kebbi ta hanyar shari'a.

Lamarin da daure kai ganin cewa da shi Gwamna Sanata Atiku Abubakar Bagudu da Janar mai murabus Bello Sarkin Yaki dukansu yan garin Birnin kebbi ne, kuma 'yan jihar Kebbi.Shin ta yaya Inyamuri ya zama uban garke a wannan sha'ani ? kenan akan neman MULKI har za a iya yin kwangilar Inyamuri domin ya jagula harkokin jihar Kebbi da sunan neman adalci a yanayi da su yan jam'iyar adawa na jihar Kebbi ba su yi ba da kan su ?.

Abin da yan jihar Kebbi suka yi zato bayan zabe shi ne irin  dattaku da tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya nuna bayan hukumar zabe ta sanar cewa ya sha kashi a hannun shugaba Buhari ya yi mubaya'a kuma ya bar lamarinshi a hannun Allah. Dalilin haka shugaba Buhari ya ci gaba da shugabanci shi kuma Goodluck ya koma kauyen shi na Otuoke cikin daraja da mutunci.

Sharhi Daga Isyaku Garba.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN