Sojin Najeriya sun kwato makamai da boko haram ta kwace a baya

Rundunar sojin Najeriya da jami'an ta ke fada da boko haram a yankin Borno sun yi nassarar fatattakar yan boko haram bayan wani gumurzu da sojin suka yi da yan boko haram din lamari da ya sa sojin suka halaka yan boko haram da dama tare da karbe makamai daga yan boko haram.

Gumurzu da aka yi tsakanin soji da boko haram ranar Talata ya sa soji bayan galaba kuma sun karbe wata tankar yaki da boko haram ta karbe daga hannun jami'an soji a baya. Haka zalika sojin sun kama tarin makamai da aka samu daga hannun boko haram.

Makamai da aka kama sun hada da Motar igwa na yaki EMBT 1 VBL , bindiga kirar AK47 1, bindigar yansanda na harba barkonon tsohuwa 1, tukunyar gass da dama, litaffan addini da dama,da buhuhuwan taki wanda ake amfani da su domin hada bom.

Sauran sun hada da motoci da aka girka masu manyan bindigogi guda 7, manyan motoci guda 4, motoci kirar Hilux guda 5, mota kirar Prado jeep 1, mota kirar gulf guda 1, Mitsubishi 4, Hiace 1 da babura da dama tare da ababen amfanin gida da dama.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN