An kama wanda ke satan wayar salula a Masallacin Juma'a na Abuja

A birnin Abuja an kama wani matashi mai shekara 27 mabaraci mai suna Bashir Adamu bisa zargin kai hari wa masu ababen hawa tare da kwace masu wayar salula ko jaka. Wanda aka kama ya ce shi ya fi kai hari ne ga Turawa ko fararen fata da ke zuwa babban Masallacin Juma'a na Abuja domin su yi Sallah.


An kama wannan dan talikin ne tare da wasu mutum biyu, ya ce ya sha yin satan wayoyin salula a Masallacin Juma'a na Abuja kuma an kama shi sau uku kuma aka gurfanar da shi a Kotu amma aka karbi belinsa daga bisani kuma ya sake aikata laifin sata a Masallaci.

Ya ce shi dai ya bayar da hankali ne wajen yi wa Turawa sata musamman ranar Juma'a yayin da suke bayar da sadaka shi kuma sai ya yi amfani da wannan dama ya sace masu wayar salula wanda yake sayarwa sai ya sayi abinci ya ci da kudin.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN