Wasika kan Buhari: Yansanda sun ba kakakin janar Babangida hakuri

Kwana uku bayan hukumar yansanda ta bayar da sanarwar neman Mr. Kassim Afegbua  kakakin tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida bisa wasu kalamai da ake zargin ya yi a kafafen watsa labarai, daga karshe dai hukumar yansanda ta ba Mr. Kassim hakuri .

Mr. Kassim ya bayyana tare da Lauyansa a hedikwatar hukumar yansanda a birnin Abuja ranar Laraba.Kakakin hukumar yansanda Moshood Jimoh ya ba Mr. Kassim hakuri kuma ya shaida masa cewa an sami rashin fahimta ne sakamakon hargitsewar bayanai tun farko.

Mr Kassim ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan fitowarsa daga ofishin yansandan cewa ya shigar da kara a wata babban Kotu a Abuja ne inda yake neman yansanda su biya shi N1b sakamakon bata masa suna domin ba a shaida masa cewa ana nemansa ba kwatsam sai aka sanar a gidajen watsa labarai cewa ana nemansa ruwa jallo.
 .
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN