Shi dai wannan Lauyan ya shekara 15 yana gabatar da kansa a matsayin Lauya, amma daga karshe ya gamu da kalubale daga wani Lauya mai suna Nnamdi Samuel Nwafor lamari da ya jawo hankalin yansanda da ke sintiri a Kotun.
Sakamakon haka ne yansanda suka tafi da Lauyan zuwa ofishinsu da ke Ojo inda ya shaida masu cewa ya yi karatun Lauya a Jami'ar Ukrain ta gabas a tsohuwar tarayyar Soviet amma ya kasa gabatar da takardar shaidar karatun.
Lauyan ya shaida wa yansanda cewa shi dan asalin garin Avodim Ubakala ne a jihar Abia.
Jami'an yansanda na sashen X-squad suna ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Tags:
LABARI