Tashin hankali a kasar Bena,Yombe ya bukaci a zauna lafiya tare da bin doka

Sakamakon wani hargitsi da ya auku a garin Bena ranar Litinin mutane da dama sun sami munanan raunuka ciki har da kariya da abin da ake kyautata zaton cewa harbin bindiga ne kamar yadda shugaban jam'iyar APC na mazabar Bena Mansur Tijjani Pako ya ce ana zargin cewa sojoji ne suka yi harbi da ya raunata tare da jikata mutanen.

Yayin da yake jawabi bayan wadanda aka raunata sun kawo masa ziyara a harabar ofishin sa bayan sun karbi magani daga Asibitin Sir Yahaya, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya yi masu jaje tare da nuna tausayi bisa yadda lamarin ya rutsa da su.

Yombe ya kuma shawarce su akan cewa su kasance masu jin tsoron Allah a duk lamarin su. Ya kuma ce su dinga kaurace wa duk wani abu da zai iya kawo tashin hankali.

Alh. Tijjani ya yi zargin cewa lamarin ya faru ne bayan dan Majalisar jiha mai wakiltar Bena ya yi yunkurin shiga gidan Sarkin Bena amma sai wasu mutane suka tozarta shi ta hanyar hana shi shiga fadar,sakamakon haka ya haddasa fitina.

Yankin Bena ya yi fama da harkar ta'addanci na masu satar Shanu ko garkuwa da mutane don karban kudin fansa a' yan shekarun baya. Amma bayan wani ingantaccen shiri na tsaro da Gwamna Atiku Bagudu ya umurta kuma Mataimakinsa Alh. Samaila Yombe ya aiwatar. Tun lokacin ne aka sami kwanciyar hankali ta fannin tsaro a yakin Bena sai yanzu da aka sami wanan matsala.


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN