Gwamnati ta kara lada zuwa N50m ga wanda ya fallasa inda Terwase yake

Gwamnatin jihar Benue ta kara kudin lada ga duk  wanda ya gano kuma ya fallasa mata wani da ake nema ruwa a jallo Mai suna Mr Terwase Akwaza, alias Ghana daga naira Miliyan 10 zuwa naira Miliyan 50. Sanarwar haka ta fito ne daga bakin kwamishinan watsa labarai na jihar Benue Lawrence Onoja jim kadan bayan kammala wani taron Majalisar Tsaro na jihar Benue ranar Juma'a 2 ga watan Febrairu.


Kwamishinan ya ce kari da aka yi a kudin ladar ya zama wajibi ganin yadda wanda ake nema ya sake sabunta salo na aikata laifi tare da mukarrabansa musamman a yankin Sankera na jihar ta Benue.

Kwamishinan ya kara da cewa Gwamnatin jihar Benue ta hana amfani da jiniya da wutan barka da zuwa. Haka zalika an hana rufe lambar mota domin an umurci jami'an tsaro cewa su kama duk mota da ta saba wa sabin dokokin ko da motar gwamnati ce.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN