• Labaran yau


  Mutum 2.277 ne aka yanke wa hukuncin kisa a Najeriya

  Kimanin mutum 2.277 ne ke jiran kisa bayan Kotu ta yanke masu hukuncin kisa wadanda ke gidajen Kurkukun Najeriya.

  Wani rahotu da New Telegraph ta fitar ya ce wadanda ke tsare a Kurkuku da suke jiran shari'a sun kai 48.702 yayin da jimilar wadanda ke rufe a Kurkuku sun kai 71.443.

  Wani bayani ya nuna cewa a 2016 zuwa yanzu an sami karin mutum 837 wadanda aka yanke masu hukuncin kisa.

  Haka zalika rahotanni sun nuna cewa kimanin mutum 254 ke jiran kisa a jihar Ogun, a bara kuwa mutum 90 ne ke jiran kisa a jihar Kaduna wadanda aka yanke musu hukunci sakamakon samunsu da laifi a kan kisa,  fashi da makami da fyade.

  A jihar Lagos akwai mutum 202 da ke jiran zartar da hukuncin kisa yayin da mutum 179 ne za'a kashe a jihar Enugu.

  Ministan harkokin cikin gida Lt. Gen Abdulrahman Dambazau ya ce akwai Kurkuku da aka gina domin ya dauki mutum 800 amma yana dauke da mutum 5.000 , Dambazau ya yi wannan bayani ne yayin da ya wakilci mataimakin shugaban kasa a wajen wani taro don gabatar da wani rahotu da hukumar gidajen yari na Najeriya tare da wata kungiyar sa kai kan jin dadin Fursunoni ta shirya a Abuja ranar Alhamis.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 2.277 ne aka yanke wa hukuncin kisa a Najeriya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama