Amitabh Bachchan ya zargi Twitter da rage yawan masoya a shafinsa

Fitaccen Jarumin wasan Finafinan India Shah Rukh Khan ya sami magoya baya miliyan 32.9 a shafin sada zumunta na Twitter sakamakon haka Dattijo uban sha'awa kuma jagoran fuskar Bollywood a zamininsa watau Amitabh Bachchan ya yi barazanar ficewa daga shafin sada zumuntar na Twitter.

Amitabh da ya yi wannan baraanar a shafinsa na Twitter ya zargi Twitter da rage yawan magoya bayansa "Twitter kun rage yawan masoya da wadanda ke biye da ni,..hahahahahahah!!! wannan ba gaskiya bane...lokaci ya yi da zan fice....na gode da kasancewa da ku...akwai kifaye da yawa a cikin teku kuma masu sha'awa".

Amma bisa ga alamu masoya da magoya bayan Amitabh sun dauki barazanar Jarumin da muhimmanci domin kuwa yawan masoyansa sun karu daga dare zuwa safe.

Yanzu fa ya rage tsakanin masoyan Shah Rukh Khan da na Amitabh Bachchan , bari mu gan wanda zai ci wannan gasar yawan magoya baya a Twitter !!!.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN