Chiyamomi su yi bayani ga majalisarsu yadda suke kashe kudi - Gwamna Bagudu

An gudanar da taron tattaunawa  tsakanin Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu da Mataimakinsa Samaila Yombe Dabai, SSG Babale Umar, shugannin jam'iyar APC na jihar Kebbi Alh. Attahiru Maccido da Mataimakinsa Alh. Abubakar Kana,Manyan jami'an Gwamnati tare da Kansiloli.

Bayan an saurari korafe korafe daga Kansilolo haka zalika daga Chiyamomi, Gwamna Atiku Bagudu ya bukaci a yafe wa juna kuma a fuskanci tsari na gano ababe da jama'a ke bukata domin inganta rayuwarsu ta hanuar bunkasa sana'ar su.

Gwamna Bagudu ya bukaci Chiyamomi su dinga yin bayani ga Majalisar kananan hukumominsu kowane wata domin tabbatar da adalci wajen tafiyar da shugabancin al'umma musamman yace Gwamnati ba za ta lamaunci wasa da hakkin jama'a ba.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN