Yansanda sun kama mace mai yin sojan gona

Dubun wata mata da take yin sojan gona a birnin Kano ya cika bayan 'yansanda sun kama ta da tufafin yansanda.Rahotanni sun ce Maryam Umar wacce aka fi sani da suna Kofar Mata ta shahara wajen yaudara.

Yansanda suna tuhumar Maryam da hada baki domin a aikata laifi, boye masu laifi da sauran ayyukan ashsha.

An kama Maryam ce a ranar 11 ga watan Febrairu kuma nan take aka gurfanar da ita a gaban Kotu ta 29 a Sabon garin Kano ranar 12 ga watan Febrairu.

Maryam dai bata sami kyakyawar shaida ba daga makwabtanta wadanda suka nuna cewa dubunta ne ya cika saboda ganin yadda take tafiyar da rayuwarta cike da zargin rashin gaskiya.

An adana Maryam a Kurkukun yansanda har sai ranar 28 ga watan Febrairu ranar da za'a sake gabatar da ita a gaban Kotu.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN