Ka san inda Abubakar Shekau ya tsere ya tafi ?

Wani kwamandan mayakan kungiyar boko haram mai suna Abdullahi Bello wanda ake wa inkiya da Abu Zainab da rundunar sojin Najeriya ta kama ya shaida wa rundunar cewa shugaban wani sashe na kungiyar ta boko haram Abubakar Shekau ya tsere zuwa Kolofata a jamhuriyar Kamaru.

Rundunar soji ta kama Bello ranar 14,Fabrairu ne yayin da yake kokarin arcewa zuwa Kano daga Bauchi kuma yana daya daga cikin kwamandodin boko haram da soji ke nema ruwa jallo . Ya shaida wa soji cewa da yawa daga cikin kwamandodin boko haram sun tsere bayan matsin lambar hare-hare daga sojin Najeriya a dajin Sambisa.

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta bayar da ladar Naira Miliyan uku ga duk wanda ya taimaka da labarin da zai kai ga kama shugaban kungiyar ta boko haram.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN