Alamomin shugaba mai rauni da yadda zai gyara tafiyarsa

Sau da yawa shugabanci kan sa rayuwar wasu mutane ya canja dare daya sakamakon dama da ake samu na wadatuwar rayuwa da iko.Wani lokaci yanayi da tsarin tafiyar da rayuwa yakan gushe a kan taragon sahihancin tafiyar da lamura da kuma setin tubalin gaskiyar rayuwa da adalci.

Ga kadan daga cikin ababe da shugaba ya kamata ya kula domin ya gyara halinsa idan yana son Duniya ta yi masa kyakkyawar shaida ko bayan ya bar shugabanci a nan gaba:

1. Idan shugaba yana yawan zagin ma'aikatansa
2.Yawan ganin lafin mutane da gangan
3.Rashin cika alkawari
4.Daukan mutane tamkar ba komai ba
5.Wulakantar da tunanin masana ilimi akan wani fanne na ilimin rayuwa
6.Rashin daukan shawara daga mutanen kirki
7.Yawan son girma kamar a bauta mashi
8.Cin mutuncin mutane ta hanyar gwale tunaninsu
9.Kirkiro wa mutane laifi da gangan
10.Tunanin cewa ya fi kowa basira ko iyawa
11.Rashin nuna gamsuwa da duk wani aikin da aka yi masa
12.Yawan ganin laifin ma'aikatansa ko mutane
13.Yawan yabon kanshi da kalamai na jarumta alhali yana wulakanta bajimtar wasu.
14.Rashin sauraron bahasi kafin zartar da hukunci.
15.Yawan ambatan laifin mutum ba tare da ambatan ababe kyawawa da mutum ya yi ba.

Yadda shugaba zai auna farin jininsa:
:
1.Idan ya iso wajen taro jama'a basu mike tasaye ba
2.Idan mutane basu damu da shi idan ya shigo taro ba
3.Idan shi da kanshi ya san baya yawan yin kyauta
4.Idan mutanen da suke zuwa wurinsa suka daina zuwa
5.Idan yana yawan samun matsala da ma'aikatansa
6.Idan baya damuwa da koken da mutane ke yi a kansa

Shawara ga shugaba:

Ka gyara tun kana da lokacin gyarawa, Duniya budurwar wawa ce, kada ka yi tunanin cewa ka san komi kuma ka iya komi saboda haka ka zama gagara badau a kaifin tunani da fahimta.Duniya za ta ba ka mamaki a lokacin da baka tunani.

Bahaushe ya ce ko shege ma yana da raranarsa balle dan halal.

Hattara da Duniya kafin Duniya ta sa ka yin hattara !!!

Daga Isyaku Garba, Mawallafi, Nazari da Binccike.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN