Faduwar tankin ruwa a Badariya, yan unguwa sun yi kira ga Gwamna Bagudu

Wani tanki da ke bayar da ruwa a wani sashe na mazauna unguwar Badariya layin Makarantar Abi  ya fadi kuma ya ruguje yau da Asuba misalin karfe 4:30 bayan tankin ya cika da ruwa.

Allah ya kiyaye domin tankin bai fadi a kan rayuwa ko dukiya ba , haka zalika lamarin bai jawo barna zahiri ba .

Babu wanda ya san musabbabin faduwar tankin ,amma wata majiya ta shaida mana cewa ana zargin cewa tankin ya fadi ne sakamakon rashin ingancin aikin tun asali wanda aka kimanta an yi shi ne shekara hudu da suka gabata.

Wani mazauni unguwar kuma makwabci ga inda tankin  yake mai suna Abubakar Tilli ya shaida mana cewa" Tankin ya fadi ne misalin karfe 4:30 na Asuba, amma Allah ya kiyaye bai fadi a kan wani abu ba".

Haka zalika mazauna unguwar sun roki Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu domin ya taimaka masu a yi masu wani sabon tankin ruwa ganin cewa wannan tanki da ya fadi shi ne ginshiki kuma madogaro na samun ruwan amfanin yau da kullum ga gidaje a wannan unguwar.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN