An fara yunkurin sasanta Kwankwaso da Ganduje ?

Wasu fitattun 'yan Najeriya sun soma shiga tsakani a rigimar da ke tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da mutumin da ya gaje shi Abdullahi Umar Ganduje.
Mutanen biyu dai ba sa ga-maciji da juna tun bayan zaben shekarar 2015, wanda tsohon Gwamna Kwankwaso ya goyi bayan mataimakin nasa wurin lashewa.

Sai dai wasu masana harkokin siyasa sun ce yunkurin tsoma bakin Kwankwaso cikin sha'anin gwamnatin Gwamna Ganduje ne ya raba kawunan tsofaffin aminan biyu, zargin da bangaren Kwankwaso ya sha musantawa.

Wata majiya da ba ta so a ambace ta ta shaida wa BBC cewa mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ne a kan gaba wurin sasanta 'yan siyasar biyu.

Majiyar ta ce ganawar da tsohon gwamnan ya yi da mataimakin shugaban kasa a lokacin da ake tsaka da rudani kan batun shirin kai ziyararsa jihar ta Kano ce ta yaye labulen yin sulhu tsakanin bangarorin biyu.

"Kazalika, a ziyarar da mataimakin shugaban kasa ya kai Kano a karshen makon jiya, ya gana da Gwamna Ganduje domin ci gaba da sulhu tsakanin tsohon gwamnan da gwamna mai-ci. Za a ci gaba da yin wannan yunkuri har sai mutanen biyu sun yafe wa juna sannan sun yi sulhu domin ci gaban jihar Kano," in ji majiyar.

Ziyarar da Rabi'u Kwankwaso ya so kai wa jihar Kano a makon jiya da kuma shawarar da rundunar 'yan sandan jihar ta ba shi ta dakatar da ziyarar sun kara dagula al'amura a tsakani bangarorin biyu.
Bangaren Kwankwaso ya sha alwashin ci gaba da shirinsa na kai ziyarar, inda ya yi zargin cewa jami'an tsaron suna nuna bangaranci a takaddamar da ke tsakaninsa da bangaren Ganduje, ko da yake 'yan sanda sun musanta zargin.

Daga bisani ne dai ya soke ziyarar, inda ya shaida wa BBC cewa ya dauki matakin ne domin kare rayukan jama'a "amma ja da baya ga rago ba tsoro ba ne."

Sai dai Kwamishinan yada labarai na jihar Mohammed Garba ya shaida wa BBC cewa "tsoro ne ya hana tsohon gwamnan kai ziyara, kuma dama na san ba zai iya kawo ziyara ba ko da wannan hatsaniya ba ta faru ba."

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Daga BBC 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN