• Labaran yau


  Yadda Gwamna Atiku Bagudu ya ke cudani da talakawansa

  Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya gudanar da ziyarce ziyarce na gani da ido irin yadda wasu ayyuka ke gudana tare da cudani da talakkawansa domin sanin yadda rayuwa ke kasancewa dasu.

  Haka zalika Gwamna Bagudu ya umarci tawagar motarsa ta tsaya inda ya sauko kuma ya zanta da wani mai sayar da Karas mai suna Isyaku Abubakar a kusa da babban makarantar koyon fasaha ta Waziru Umaru da ke garin Birnin kebbi.

  Gwamna Bagudu ya ba Isyaku kyautar kudi domin tallafi don ya bunkasa sana'arsa. Haka zalika Gwamnan ya ce Gwamnatinsa na duba yiwuwar samar da yanayi na sarrafa Karas domin samar da yanayi da al'umma za su amfana. Gwamna Bagudu ya kuma ziyarci gidan da ake ajiye kangararrun yara inda ya ya yi umarni da a samar da ingantaccen ruwan sha kuma a inganta yanayin gidan da rayuwan yara da ke cikin gidan.

  Ya kuma kai ziyarar gani da ido aikin hanya na Badariya-Kola-Wuro Maliki-Zuguru da kuma aikin hanyoyi a garin Kola.Daga bisani Gwamnan ya kai ziyara a Makabartar Musulmi ta Sabuwar babban Bankin Najeriya inda ya yi wa mamata addu'a tare da wasu manyan jami'an Gwamnatinsa.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda Gwamna Atiku Bagudu ya ke cudani da talakawansa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama