• Labaran yau


  An cafke Lauyan bogi da ke tsaya wa wasu a Kotu

  Wani mutum mai suna Omoniyi Vacoster ya fada hannun yansanda a jihar Ogun bayan an zarge shi da yin sojin gona na kasancewa Lauya.Wannan ya biyo bayan wani koke da wani mai suna Omomehin Oluwatoyi daga kungiyar Lauyoyi na jihar Ogun ya gabatar wa hukumar yansanda cewa wanda ake zargin yana gabatar da kansa a matsayin Lauya alhalin ba gaskiya bane.

  Mai magana da yawun hukumar yansanda na jihar Ogun Abimbola Oyeyeyemi ya ce wanda ake zargin ya ce bai taba zuwa makarantar koyon aikin Lauya ba lokacin da ake gudanar da bincike.

  Kakakin yansanda ya ce za su gurfanar da Omoniyi a gaban Kotu da zarar sun kammala bincike.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An cafke Lauyan bogi da ke tsaya wa wasu a Kotu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama