Ziyarar ta'aziyar Sarkin Zuru ga Gwamna Atiku Bagudu - Hotuna

Mai Martaba Sarkin Zuru Alh. Muhammadu Sani Sami ya kai ziyarar  ta'aziyya ga iyalan gidan Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu sakamakon rasuwar Gwaggon sa a unguwar Kofar Kola da ke garin Birnin Kebbi ranar Alhamis.

Sarkin na Masaurautar Zuru ya roki Allah ya gafarta wa mamaciyar ya sanyaya kuma ya karbi bakoncinta cikin rahamarsa.

Kafin ziyarar ta'aziyar, Basaraken ya kai ziyarar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Gwandu Alh. Iliyasu Bashar a fadar sa da ke garin Birnin kebbi.

Daga cikin wadanda suka mara wa Sarkin baya a wajen ziyarar sun hada da Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai, 'yan majalisar Sarkin Zuru, shugaban karamar hukumar Zuru Alh. Muhammed Kabir Abubakar, SSA Abdulrahman Manga da sauran jama'a.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN