Gwamnatin jihar Kebbi ta dakatar da Dr. Sahabi Adamu B. Yauri daga aiki

Gwamnatin jihar Kebbi ta amince da dakatar da Dr. Sahabi Adamu Birnin Yauri babban Sakatare na Scholarship Board bisa zargin aikata ba daidai ba.

A wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na Gwamnatin jihar Kebbi Abubakar Mu'azu Dakingari ya fitar, sanarwar ta ce dakatawar na da nassaba da zargin aikata ba daidai ba da kudaden bibiya na dalibai a jami'ar Bharati Deemed da ke Pune a kasar India.

Sanarwar ta kara da cewa an dauki matakin ne domin a sami sukunin gudanar da cikakken bincike.

Sanarwar ta ce an umarci Sakataren ya mika ragamar harkoki ga babban Darakta na ma'aikatar.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN