• Labaran yau

  Yadda barayi suka like bakin tsohuwa yar shekara 89 da super glue kafin su yi sata

  Yansanda a jihar Edo sun cafke wasu mutane biyu wadanda ta ce sun yi amfani da super glue suka manne bakin wata tsohuwa  Imasogbonre Enahoro 'yar shekara 89 da diyarta  Marylyn Ajibola saboda kada su yi itu don samun taimako lokacin da 'yan fashin suke sata a gidan a kauyen Igueben ranar 20 ga watan Nuwamba 2017 inda suka saci kayaki da dama tare da mota kirar Toyota Camry.

  Wadanda aka kama su ne Kingsley Odion da Tosin. Bayanai sun nuna cewa bayan sun shiga gidan sai suka daure kowa, amma diyar tsohuwar watau Tosin ta ci gaba da magana, dalili da ya sa suka yi amfani da super glue suka manne bakinta.

  The Nation ta ruwaito cewa Marylyn ta shaida daya daga cikin 'yan fashin wanda ta ce shi ne ya mari mahaifiyarta daga bisani ya daure bakunansu. Ta yi wannan bayani ne a hedikwatar 'yansanda a garin Benin.

  Kingsley daya daga cikin wadanda aka kama ya ce shi dalibi ne a Federal polytechnic Auchi, ya kara da cewa lokacin da suka shiga gidan tsohuwar bata da kudi , amma sun sami N7,200 a cikin motar da suka sace wacce daga bisani aka gano ta a jihar Osun.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Yadda barayi suka like bakin tsohuwa yar shekara 89 da super glue kafin su yi sata Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama