Yansanda 3 sun fuskanci koran kare daga aiki bayan sun kashe wani saurayi

Hukumar 'yansanda na jihar Lagos ta kori wadansu jami'an 'yansanda guda uku daga aiki bayan hukumar ta tuhumesu bisa dokokin aikin 'dansanda kuma aka same su da laifin kisa a ranar 11/01/2018 da misalin karfe 9:30 na dare.

Wadanda aka kora sun hada da 25759 Sgt. Osaseri Saturday, 35 9075 Sgt. Segun Okun, 496833 Cpl. Adekunle Oluwarotimi wadanda ke aiki a rundunar 'yansanda na Amukoko a birnin Lagos.

Rahotanni sun nuna cewa yansandan sun buda wuta da bindiga akan wasu yara wadanda ke wasa da ababen fashewa da ake kira knockout da dare a unguwar Ifelodun a Amukoko ranar 11/01/2017 sakamakon haka wani saurayi ya mutu yayin da wani saurayin ya jikata.

Kwamishinan 'yansanda na jihar Lagos CP. Edgal Imohimi ya umarci shugabannin 'yansanda Area Commanders da DPO's cewa wajibi ne su tabbatar cewa 'yansanda da ke aiki karkashinsu sun bi ka'idar dokar amfani da makami na 'yansanda kamar yadda dokar ta 237 ta tanada.

CP. Edgal ya kara da cewa hukumar 'yansanda na jihar Lagos ba za ta lamunce kisan jama'a da basu ji basu gani ba daga kowane jami'in 'dansanda.

Bayanai sun nuna cewa bayan koran 'yansandan, hukumar za ta gurfanar da su a gaban Kotu mako mai zuwa yayin da aka kai takardar wannan karar ga sashen DPP na jihar Lagos domin neman shawara.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN