• Labaran yau

  Rashin cin jarabawa: Hedimasta ya sha duka a hannun uwayen dalibai (Hotuna)

  Shugaban wani makarantar firamare watau hedimasta mai suna Yonah Oyugi na Urudi primary school ya sha dan karen duka a hannun uwayen dalibai a Kisumu ta arewa a kasar Kenya bayan iyayen dalibai sun zarge shi da zama sanadi bayan rinjayen daliban makarantar sun fadi jarabawa.

  Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne yayin da ake wata tattaunawa tsakanin shugabannin makarantar da uwayen dalibai inda bangarorin biyu suka dora wa juna laifi.

  Amma lamari ya rikide ne bayan uwayen dalibai da ke wurin tattaunawar sun yi zargin cewa hedimasta Yonah Oyugi ya zage su tare da yaransu wadanda dalibai ne a makarantar. Sakamakon haka wasu daga cikin uwayen dalibai suka afka wa hedimasta da duka da ya kai ga yi masa rauni.

  'Dalibi da ya fi maki a jarabawa na shaidan kammala karatun firamare na kasar Kenya a makarantar shi ne wanda ya ci maki 238 a cikin 500 daga cikin dalibai 27, yayin da wasu dalibai hudu ne kawai suka sami maki fiye da 200, daya kuma yana da maki 87.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Rashin cin jarabawa: Hedimasta ya sha duka a hannun uwayen dalibai (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama