• Labaran yau

  Babban magana ! miji ya yi wa mahaifiyar matarsa ciki

  Isyaku Garba |

  Wani kafinta mai suna John Ulaha dan shekara 45 ya shiga matsanancin damuwa tare da nadama bayan ya yi wa surukarsa watau mahaifiyar matarsa ciki a karamar hukumar Awe a jihar Nassarawa, amma ya sha alwashin cewa zai yi iya abin da zai iya domin ganin cewa an zubar da cikin.

  Saturday Sun ta ruwaito cewa matarsa tana zaune a Lafia na jihar Nassarawa wajen da take kula da shagonta na kayakin masarufi yayin da shi kuma yana aikin kafinta. Ma'auratan biyu suna noma a garin Awe, sakamakon haka suka dauki hayan ma'aikata domin su yi masu noman.

  Amma bayan dokan hana kiwo da aka yi a jihar Benue wanda ya sa Fulani suka yi kaura zuwa jihar Nassarawa sakamakon haka gonaki da dama suka salwanta, wannan ya sa matar John ta gayyato mahaifiyarta domin ta taimaka wa mijinta girbe doya da masara da suka noma.

  Bayan wata uku sai ciki ya bayyana ga mahaifiyar matar John watau Mrs. Ashetu Igbesu 'yar shekara 42 a wani lamari da ya kawo rudani bayan ta ce cikin na mijin diyarta ne.

  Ita diyar nata watau Victoria, ta ce ita lamarin ya bata matukar mamaki yadda soyayya ya shiga tsakanin mahaifiyarta da mijinta har ya kai ga samun ciki.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Babban magana ! miji ya yi wa mahaifiyar matarsa ciki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama