• Labaran yau

  Majalisar agaji na Izala a Shanga ta kammala taron bita

  Daga Sani Musa Saminaka |

  Majalisar Agaji na Izala ta karamar hukumar mulki ta Shanga ta kammala taron bita da ta shirya a garin Saminaka tun daga ranar 04/01/2018 zuwa Lahadi 07/01/2018.

  'Yan Agajin sun koyi abubuwa daban-daban ta fuskar aiki da gabban jiki da kuma mu'amala mai kyau a cikin al'umma.

  Kamar yadda shugabannasu Alh.Muhammad Aliyu girom masa ya tabbatar mana.

  Wannan taro na rufewa da suka yi ya samu bakoncin mataimakin babban Darakatan Agaji na jiha Alh.Muhammad Bello Umar Koko da saura makarabbansa a mataki na jaha. Haka zalika shugaban Majalisar malamai na shanga shima ya hallaci taron , inda ya gabatar da wa'azinsa zuwa 'yan agaji akan yin aiki don Allah tare da jin tsoronsa acikin kowace irim mu'amala.

  Shugaban kungiyar na karamar hukumar Alh.Muhammad Bello Ganwo ya yi godiya ta musamman ga babban daraktan agaji na jaha akan yunkurin da ya yi na ganin cewa ya hallarci wannan taron , amma damar bata samuba saboda wani dalili , sai ya turo mataimakinsa da sauran makarabbansa saboda muhimmancin taron a wurinsa.

  Ya kuma yi godiya zuwa ga 'yan agaji akan hakurin da suka yi da juna tsawon kwana uku ba tare da wata tsangwama ba.

  Daga karshe hugaban ya kara jan hankalin su a kan su yi kokari su zama mutanen kirki a cikin al'umma kada su zama akasin haka
  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Majalisar agaji na Izala a Shanga ta kammala taron bita Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama