Mutum 72 sun haukace a Zamfara sakamakon shaye-shaye

Matsalar shaye shaye ya zama ruwan dare a jihar Zamfara lamari da ya haifar da haukacewan mutum 72 a cikin shekara 3 da suka gabata. Wani babban jami'i na rundunar kiyaye sha da mu'amala da miyagun kwayoyi na kasa NDLEA Mr Ladan Hashim ne ya fadi haka a garin Gusau ranar Laraba.

Mr Ladan ya ce shaye shaye a tsakanin matasa da 'yan mata ya zama abun tsoro ganin yadda lamarin ke karuwa a tsakanin matasa.

Ya ce a 2015 mutum 27 sun haukace haka zalika a 2016 da 2017 mutum 45 sun sami tabin hankali ciki har da mata 5. Ya kara da cewa lamarin ya yi kamari a tsakanin 'yan mata da ke karatu a manyan makarantu a cikin fadin jihar.

A wani shiri na Radiyon FM a garin Gusau, Mr Ladan ya ce an sami matsala inda wata yarinya ta koya wa mahaifiyarta yadda ake shan Syrup watau maganin barci da ke gusar da hankalin mutum, ya kara da cewa lamarin ya yi muni domin yanzu haka hatta a gidajen matan aure ana zukan Syrup.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN