• Labaran yau


  Ko ka san an fi sha'awar mata masu murdandun jijiyoyi bisa ga sirara ?

  Sakamakon wani bincike da aka gudanara a Jami'ar Missouri a birnin Kansas na kasar Amurka ya nuna cewa an fi sha'awar mata masu murdadden jiki bisa ga zukakkun mata ko lange-lange mata.

  Wasu masu bincike ne suka gudanar da binciken a Jami'ar ta Missouri, sun fara ne da duba hotunan mata da jama'a suka fadi ra'ayinsu kasancewa mafi sha'awa kuma sun gano cewa mata masu murdaddun jiki ne aka fi zaba bisa ga mata sirara ko lange-lange.

  Daga cikin binciken, masana sun nazarci hotunan wadanda suka yi takaran sarauniyar kyau na kasar Amurka daga shekara ta 1999 zuwa 2013 kuma sun gano cewa an fi zaben mata masu murdaddun jijiyoyi a matsayin sarauniyar kyau.

  Haka zalika wasu nau'in nazarce nazarce da bincike da masu binciken suka gudanar ya nuna tabbacin ikirarin nasu kamar yadda suka gabatar.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ko ka san an fi sha'awar mata masu murdandun jijiyoyi bisa ga sirara ? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama