Jami'in NSCDC ya harbe mai gadi da bindiga

Wasu bayin Allah sun ceci rayuwar wani Mai gadi mai suna Chizorom Anayo wanda ke gadi a Hotel na East Gate da ke garin Owerri na jihar Imo bayan wani jami'in tsaro na NSCDC ya harbe shi da bindiga ranar Talata.

Majiyar mu ta ce Mai gadin dan shekara 43 haifaffen karamar hukumar Ohaji/Egbema ne a jihar Imo.Wani jamai'in NSCDC da ke cikin tawagar Kwamishinan muhalli na jihar Imo ne ya harbe shi da misalin karfe 8:20 na dare .

Punch ta ruwaito cewa Kwamishinan tare da tawagarsa sun biyo wani mai tuka Keke napep ne bisa doka da Gwamnati ta fara amfani da shi kan masu Keken napep. Shi kuma mai keke ya ruga ya shiga cikin harabar Hotel din domin ya sami mafaka.

Bayan sun kama shi a cikin Hotel din sai suka kama dukansa, ganin dukan ya yi yawa sai Mai gadin Hotel Chizoron ya bukaci cewa su daina dukansa hakanan domin kada su kashe shi a cikin Hotel din, nan take jami'in NSCDC ya mari mai gadi kuma ya sa bindiga ya harbe shi a kafa.

Mai gadi ya kwanta a Asibitin yansanda inda akayi masa tiyatan cire harsashi.Tuni dai mai gadi ya kai kara Chaji ofis kuma tuni 'yansanda suka fara neman jami'in NSCDC da ya yi harbin.

Kakakin hukumar yansanda na jihar Imo Andrewa Enwerem ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce suna gudanar da bincike.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN