Kotu ta dage sauraron shari'ar Gwamnan Kebbi zuwa 6 ga Fabrairu 2018

Tun da misalin karfe 11:00am na yau (30/01/2018) magoya bayan jam'iyyun siyasar APC da PDP suka yi dafifi a bakin Babbar kotu dake nan Abuja domin ganin yadda zata kaya a shari'ar da aka fafata jiya kuma aka dage zaman har yau domin ci gaba da saurare, 

Alkalin Babbar kotun ya nemi ci gaba da shari'ar da misalin karfe 12:15pm, sai dai kash lauyan wanda suka shigar da karar bai zo ba, saboda haka sai yaci gaba da shari'o'in dake gaban sa. 

Da misalin karfe 1:47pm,alkalin ya sake waiwaye akan shari'ar sai akayi sa'a kuwa lauyan ya shigo har ya zauna, saboda haka ba tare da bata lokaci ba, sai Barr. Attahiru Maccido shugaban jam'iyyar APC na jihar Kebbi ya Mike tsaye domin karɓa umarnin kotu da yake a cikin karar har da partin sa, daga nan lauyoyin kowane bangare ya shiga gabatar da kansa kamar yadda al'adar kotu, ta tanada.
Daga nan sai Alkalin Babbar kotun ya umurci SAN. Y. C. Mai kyau, da yaci gaba da bayanan sa da ya fara tun jiya masu nuni da suka akan shaidar da lauyan PDP ya gabatar a matsayin a basu kujerar Gwamnan jihar Kebbi. 

Lauyan mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sen Atiku Bagudu Abubakar ya fara caccakar hujjojin lauyan PDP da cewa, shaidar da aka gabatar tanada illoli kamar haka, ya bayyana cewa :
- shaidar dai ba ingantacciya bace (ba original copy bace) aka gabatar ga kotu ba, 

- shaidar da aka gabatar, kundi ne na Al'umma, bashi da nasaba da shari'a ko kuma mashari'anta,

- Akwai tunka da walwala acikin kwanan watan da aka gabatar a wajen bada shaidar. 

-Akwai wata tunka da walwala kuma a wurin takamaiman wurin da akace abin ya faru kaman yadda aka gabatar a matsayin shaida a gaban kotu, 

- Babu sahihiyar hujja data bayyanawa kotu hanyar da aka bi aka samo wannan takardar daga Amerika. 

- Babban mai shari'a na jc Ireland da aka rubuta sunan shi acikin shaidar da aka gabatar babu sa hannun sa balle hatimin sa. 

Da sauran hujjojin da ni dan social media bazan iya fahimtar suba Saboda ba layina bane. 

Daga nan sai Alkalin ya bukaci lauyoyi masu wakiltar Jam'iyyar APC da kuma INEC suma suyi tsokaci akan wannan batu, sai nan take suka ce sun amince da duk bayanin Babban lauya SAN. Y. C. Mai kyau yayi, shi kuma Alkalin Babbar kotun ya yi duba da kulewar lokaci sai ya dage zaman kotu zuwa ranar Talata 06/02 /2018 da misalin karfe 1:00pm idan Allah ya kaimu. Inda kai tsaye za'a baiwa lauyan PDP dama domin ya kare suka da ragargazar hujjojin sa da akayi a wannan makon.

Adamu Attahiru
Northwest chairman
APC social media.


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN