Kotu ta yanke wa barawon buhun wake mai nauyin 15k hukuncin bulala 6

Wani Alkalin Kotu a Karmu na birnin tarayya Abuja ya yanke wa wani mutum mai suna Abubakar Sadiq mazauni Gwagwa karmo hukuncin bulala shida bayan ya amsa laifisa na satan wani buhun wake mai nauyin 15k.

Alkalin Kotun ya ce ya yi sauki wajen yanke wa Kabiru hukunci ne saboda ya amsa laifinsa ba tare da bata wa Kotu lokaci ba.

Mai gabatar da kara Mr. Dalhatu Zannah ya gaya wa Kotun cewa wanda aka yi kara Kabiru ya shiga shagon wani mai suna Abdullahi Mohammed mazauni garin Jiwa a birnin Abuja ba tare da izininsa ba kuma ya saci buhun wake ranar 23 ga watan Janairu.

Bayan wanda aka yi wa sata ya kai kara a caji ofis na 'yansanda sai suka kama Kabiru a garin Agura yayin da yake kokarin sayar da buhun waken, kuma yayin gudanar da binciken yansanda ne Kabiru ya amsa laifinsa kafin ya gurfana a gaban Kotu inda a nan ma ya amsa laifinsa.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN