• Labaran yau

  Kalli yadda motar tilera ta take wannan matashi (Hotuna)

  A garin Ngwalangu na karamar hukumar Ohozara a jihar Ebonyi wani matashi ya gamu da ajalinsa bayan motar tilera da yake kwance a karkashinta ta take shi sakamakon wani hatsari da ya faru ranar Alhamis.

  Rahotanni sun nuna cewa matashin da ya mutu ya kasance a cikin matuka tileran ne wadda ta tsaya a gefen titi, shi kuma bawan Allah sai ya kwanta a karkashinta domin ya huta ,daga bisani sai barci ya kwashe shi.

  Kwatsam sai wata babban mota ta kwace ta nufato wannan tilera da matashin ke kwance a karkashinta ta yi karo da ita, sakamakon haka motar tilera ta matsa baya ta take matashin wanda ya mutu nan take.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Kalli yadda motar tilera ta take wannan matashi (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama