Kotu ta daure matar da ta yi yunkurin sayar da jariranta 2 shekara 10 a kurkuku

Babban Kotun Majistare a garin Katsina ta yanke wa Salima Lawal matar da ta yi yunkurin sayar da jariranta biyu a farkon watan Disamba na 2017 akan kudi N350,000 hukuncin daurin shekara 10 a Kurkuku ko ta biya taran N10,000.

Ranar Laraba data gabata ne Alkalin Kotun Nuradeen El-ladan ya yanke mata wannan hukuncin.Nurudden ya ce ya yi mata sassaucin hukuncin ne sakamakon nadama da mahaifiyar ta nuna tare da yin la'akari da irin matsanancin talauci da ya kai ta ga yin wannan yunkurin, haka zalika ta share lokaci tare da jariranta 2 a gidan yari.

Idan baku manta ba, Salima ta tuntubi wani mutum ne da zance yunkurin sayar da jariran inda ta taya mashi cewa ko zai saye jariran nata a kan kudi N350,000 a garin 'Dan dume da ke jihar ta Katsina a farkon watan Disamba na 2017. Sakamakon haka shi mutumin ya garzaya ya shaida wa 'yansanda da suka zo daga bisani suka kama Salima. 

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN