• Labaran yau


  Jami'an tsaro sun kashe kusurgumin dan ta'adda

  Rundunar tsaro na DSS tare da hadin gwuiwar jami'an sojin Najeriya sun yi nassarar halaka  Oluchi Igwedibia alias Obata Osu kanin Don Wanny wadanda dukanninsu 'yan ta'adda ne masu garkuwa da mutane domin karban fansa a jihar Rivers.

  Obata yana cikin mutum 'yan kungiyar asiri 32 da mahukunta ke nema ruwa jallo a jihar ta Rivers.

  Jami'an tsaro sun kashe Obata ne a garin Sabo Iyakpe na yamma a jihar Edo ranar Asabar 28/2/2018 bayan wasu bayanan sirri da aka samu daga DSS.

  Shi dai wanna talikin ya taka rawa wajen kisan wadansu masu ibada da ke dawowa daga Chochi ranar sabuwar shekara a jihar Rivers.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jami'an tsaro sun kashe kusurgumin dan ta'adda Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama