Fiye da mutum 267.000 na PDP sun koma APC a jihar Kebbi - Hotuna

Fiye da mutum 267.000 ne suka canja sheka daga jam'iyar PDP zuwa jam'iyar APC a jihar Kebbi wanda suka hada da kuguwa ta baya yayannan na dawowar tsohon Gwamnan jihar Kebbi Alh. Sa'idu Nasamu Dakingari tare da mataimakinsa da sauran manyyan jami'an Gwamnati a zamaninsa zuwa jam'iyar APC mai muki a Najeriya da jihar Kebbi.

Filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi mazaunin Gwamnatin jihar Kebbi ya cika makil da magoya bayan jam'iyar  ta APC tare da wadanda suka canja sheka daga jam'iyar PDP zuwa APC a wani biki na wankan tsarki da shugaban jam'iyar na APC na kasa tare da na jihar Kebbi Alh. Attahiru Maccido   karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya gudanar.


Duk wani babban jami'in Gwamnatin jihar Kebbi ya halarci taron, haka zalika manya da kananan 'yan siyasa a fadin jihar Kebbi sun hallara.

Tsohon gwamna Alh. Sa'idu Dakingari ya ce sun dawo jam'iyar APC ne sakamakon adalcin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wajen shirye shiryensa da suka kawo ci gaba,dogaro da kai tare da samar da tsaro. Haka zalika ya ce adalci, da ayyuka tukuru na ciyar da jihar Kebbi gaba da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ke yi ya sa suka dawo jam'iyar APC.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun laranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN