APC a Kebbi ta karbi Dakingari da jama'arsa daga PDP zuwa APC - Hotuna

Ranar Asabar ne tsohon Gwamnan jihar Kebbi Alh. Sa'idu Nasamu Dakingari ya jagoranci wasu manyan jami'an Gwamnati a zamaninsa tare da dubatan jama'a inda suka canja sheka zuwa jam'iyar APC wanda Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu tare da Mataimakinsa Alh. Samaila Yombe Dabai, da sauran manyan jami'an Gwamnati suka yi a filin wasa na Haliru Abdu da ke garin birnin kebbi.

Dubun dubatan magoya bayan jam'iyar PDP ne suka canja sheka zuwa jam'iyar APC musamman a wannan guguwar ta canjin sheka karkashin tsohon Gwamna Sa'idu Dakingari.

Wani mai fashin bakin siyasa Alh.Kabiru Inuwa Sani wanda ke zaune a garin Jega na jihar Kebbi ya shaida mana cewa "Wanan ya nuna cewa karshen jam'iyar PDP ya gabato kenan a jihar Kebbi, Alh Kabiru ya kara da cewa canjin shekar wadannan jigajigan ginshikin jam'iyar PDP ba karamar illa ta yi ba a tsarin jam'iyar haka zalika lamarin ya kawo alhairi ga jam'iyar APC".

Dakingari ya ce tun lokacin da ya sauka daga mukamin Gwamnan jihar Kebbi babu wanda ya sake jin kalamansa dangane da harkokin siyasa. Haka zalika sun dawo jam'iyar APC ne ba tare da gitta wani sharadi ba.

Ya kara da cewa "Mun dawo jam'iyar APC ne sakamakon irin namijin kokari da shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Atiku Bagudu ke yi na bunkasa rayuwa tare da kawo ci gaba ga 'yan Najeriya tare da la'akari da inganci da aka samar ta fannin tsaro.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN