Barayi sun banka wa 'dan shekara 12 wuta don ya gane su - Hotuna

Wani yaro mai shekara 12 mai suna Ojonugwa ya gamu da ibtila'i bayan wasu bata gari sun banka masa wuta da ransa a garin Ogogu na karamar hukumar Olamobaro a jihar Kogi saboda wayan salula.

Shi dai wannan yaro ya shaida wadanda suka yi satan wayaoyin salula ne , sakamakon haka barayin suka dora shi a kan babur suka tafi da shi wani waje mai nisa. Rahotanni sun nuna cewa sun bukaci yaron ya kwanta kuma nan take ya bi umurninsu.

Daga bisani sai suka zuko man fetur daga babur suka watsa ma yaron sai suka banka masa wuta ,yaron ya yi ta birgima sai ya tsunduma a cikin wani drum da ke da ruwa a ciki.

Ganin haka ya sa barayin suka yi zaton cewa yaron ya mutu sai suka tafi suka bar wajen.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN